Malam Umar Namadi ya ce shirin na da nufin samar da miloniyoyi 150 a tsawon wa'adin mulkinsa.
Yayin da yake jawabi a wurin ƙaddamar da bai wa mata 1000 jari domin dogaro da kansu, gwamnan ya ce shirin na daga cikin sauye-sauyen tattalin arziki da ci gaba da gwamnatinsa ta ɓullo da su.
"Gwamnatinmu ta fahimci muradun al'ummarmu, don haka muna buƙatar tallafa musu domin ba su damar cimma muradunsu''.
Gwamnan ya kuma yi kira ga mata kan irin rawar da za su iya takawa wajen haɓakar tattalin arzikin jihar.
"A bayyane take cewa mata na iya bakin ƙoƙarinsu wajen raino tare da inganta sana'o'i, don haka za mu ci gaba da ƙarfafa musu gwiwwa, muna sane da irin gudunmowar da suka ba mu a lokacin yaƙin neman zaɓe da bayan zaɓe'', in ji gwamnan na Jigawa.