Hukumar Kwastan mai kula da yankin Adamawa da Taraba ta kama fatun jaki, man fetur da sauran kayayyakin da aka yi fasakwaurinsu na kimanin Naira miliyan 19.4 a watan Agusta.
Kwanturolan hukumar, Salisu Kazaure ne ya sanar da haka yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Yola a yau Alhamis.
Ya ce kayayyakin da aka kama sun hada da danyun fatar jaki guda 200 da kuma motar da ake safarar su ta barauniyar hanya, da kuma buhu 127 na shinkafar kasar waje mai nauyin kilogiram 50.
A cewarsa, sauran kayan da aka kama sun hada da lita dubu 12,355 na man fetur a cikin jarkoki.
"Hukumar munba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da fasakwaurin da ake tafkawa a hanyoyin ruwa da kuma kasa," in ji shi.
Ya yabawa hedkwatar hukumar ta Kwastan bisa gaggarumin tallafin kayan aiki wanda a cewarsa hakan ya baiwa jami’an hukumar damar gudanar da aikin yadda ya kamata.
Ya kara da cewa "Za mu ci gaba da yin hadin gwiwa tare da hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki don magance wannan mummunar ta'ada," in ji shi