Hukumar kula da harkokin ilimi ta ƙaramar hukumar Kano Municipal ta gudanar da babban taron karrama ƙungiyar kafintoci ta kano tare da wasu muhimman mutane da sukai aiki tuƙuru wajen ganin sun tallafawa bangaren ilimi a ƙaramar hukumar.
Taron wanda aka gudanar a ofishin sakataren ilimi na hukumar Mal. Abdulƙadir Kabara inda ya bayyana taron matsayin godiya da nuna farin ciki bisa aikin gina makarantar Gandu da waɗannan kungiyoyi sukai kuma suke kan yi a maimakon a zubawa gwamnati ido har sai sanda ta waiwayi makarantar don gabatar da aikin daya kamata.
Shugaban makarantar Gandu ya bayyana cewa makarantar na daga makarantu da suke da ƙarancin cigaba na mallakar kayayyakin aiki na malamai dana ɗalibai wanda ya haɗar da banchina, alli da sauran su, amma wannan ƙungiya ta kafintoci da wasu cikin manyan mutane sun taimaka ciki har da ƙungiyar tsaffin ɗalibai ta makarantar ƙarƙashin shugaban su Ibrahim Hussaini Abubakar Danlawan.
Headmastan ya ƙara da cewa waɗannan ƙungiyoyi sun maida makarantar sabuwa kuma abar alfahari a cikin ƙaramar hukumar su dama jihar kano baki ɗaya.
A jawabin sa shugaban ƙungiyar kafintoci Cmr. Abubakar Yusuf Ahmad ya bayyana cewa ba a iya nan zasu tsaya wajen gyarawa makarantu ababen zama ba suna da aniyar cigaba da wannan aikin alkhairi ga ɗaukacin ƙananun hukumomin jihar kano baki ɗaya duk domin a samarwa da al'umma cigaba ba sai an jira gwamnati tayi ba.
Shima Jagoran Al'umma gatan makaranta na ƙaramar hukumar Alh. Umaru ya bayyana wannan rana matsayin ranar farin ciki bisa yadda aka karrama wannan mutane don yabawa aikin taimako da sukai wanda zai zama ƙwarin gwiwa gare su.
A ƙarshe Shugaban Ƙungiyar tsaffin ɗalibai ta (GANDU OLD BOYS ASSOCIATION) Ibrahim Hussain Abubakar Ɗanlawan ya bayyana yadda suka fara wannan aiki na gina makarantar Gandu dama abubuwan da suka cimma wanda ya haɗar da gyaran azuzuwa da siyan kayayyakin amfani masu muhimmanci ga malamai dama ɗaliban baki ɗaya.