Kungiyar Injiniyoyi ta ƙasa reshen jihar kano wato (Nigeria Society Of Engineers) NSE, ta gudanar da taro kamar yadda ta saba duk ƙarshen wata.
Taron na wannan wata ya dubi yadda za'a ƙirƙiro da sabbin hanyoyin inganta gine-gine dama hanyoyi wanda gwamnati ke ɗaukar nauyi dama masu hannu da shuni.
Engr. Ibrahim Usman Dederi shine shugaban ƙungiyar reshen jihar kani ya kuma bayyanawa manema labarai cewa ''mun tattauna abubuwa da yawa musamman yadda injiniyoyi zasu baiwa gwamnatocin jihohi gudunmawa ta yadda za'a gabatar da aiki mai inganci ba tare da samun matsa wadda ka janyo kashe kuɗi a banza ba.
ya baiwa kungiyar gudunmawa ta musamman ga ƙungiyar wanda ya bayyana cewa ba don komai ya baiwa ƙungiyar NSE gudunmawa ta musamman ba face don ganin yadda suke iya ƙoƙarin su don ganin sunyi aikin alkhairi wanda zai ciyar da al'umma gaba.
Engr. Rabi'u Haruna