Gwamna Babajide Sanwo Olu shi ya jagoranci kaddamar da jirgin, inda gwamnan ya shiga jirgin daga tashar Marina zuwa Mile 2.
Gwamnan ya buƙaci ƴan jihar ta Legas da su taimaka wajen kula da hanyar jirgin ƙasan, duk da cewa gwamnatinsa ta sanya matakai na yin hakan.
Ya ce an sanya kyamarorin tsaro sama da 300 a faɗin titin jirgin domin ba shi kariyar da ta kamata.
An kiyasta cewa jirgin zai iya ɗaukar fasinjoji tsakanin 150,000 zuwa 175,000 a kowace rana.
BBC