Kotun sauraron kararrakin zaɓen yan majalisa, tayi fatali da ƙarar da Injiniya Umar Abdullahi Umar (Abba Ganduje) ya shigar a gaban ta,ya na ƙalubalantar nasarar zaɓaɓɓen dan majalisar wakilai ta ƙasa, mai wakiltar ƙananan hukumomin Tofa, Dawakin Tofa da Rimin Gado, Hon Tijjani Abdulƙadir Joɓe.
Hakazalika kotun ta ci tarar Abba Ganduje, ya biya kuɗi N200,000 ga dukkan bangarori uku da yake ƙara, wato Tijjani Abdulkadir Joɓe, Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, da kuma jam'iyyar NNPP.