An bayyana juyin mulkin daya faru a Gabo a matsayin babbar cikas ga dimokaraɗiyya a Nahiyar Africa ~ Mal. Usman Mujittaba
Gabon Ƙasa ce a Nahiyar Afirka wadda ta wayi gari a hannun Sojojin ƙasar. Mal. Usman Mujittaba Shugaban Sashen tsare-tsaren karatu a kwalejin Annur dake Rangaza ƙaramar hukumar Ungogo wanda masani ne a kan al'amuran yau da kullum ya bayyana cewa Dimokaraɗiyya a kowane hali ta cancanta a kowace ƙasa a duniya musamman a Nahiyar Afirka wadda ke ɗauke da ƙasashe masu tasowa musamman a fannin tattalin arziƙi.
Mal. Usman ya ƙara da cewa a mulkin dimokaraɗiyya ne kaɗai ake iya cimma muradan cigaban ƙasa mai ɗorewa kuma babban abun ƙyama a mulkin soja shine babu wani da zai iya fitowa a ƙasa ya faɗi ra'ayi ba baki ko yayi zaben don canza gwamnati.
A ƙarshe Mal. Usman yace Najeriya na cikin yanayin da kowace ƙasa zata so kasancewa a ciki musamman fannin faɗar ra'ayi da kuma canza gwamnati a duk lokacin da Talaka yaso muddin gwamnatin ta kasa cika musu alƙawarin data ɗaukar musu ko kuma ta bullo da sabon lamarin da bai yiwa ƴan ƙasar daɗi ba.