Jagoran juyin mulki a Gabon, Janar Brice Oligwe Ngwema, ya ce za su mayar da hankali wajen ƙarfafa mulkin dimukuradiyya a ma'aikatun kasar.
Ngwema ya ce za a sake gyara su da kyakkyawan tsari da inganci, sannan juyin mulkin da suka yi wa gwamnatin Shugaba Ali Bongo a ranar Laraba na wucin-gadi ne.
Tun da fari a jiya Juma'a, 'yan adawa a Gabon sun zargi sojoji da ƙin nuna alamar shirin miƙa mulki ga gwamnatin farar hula.Mai magana da yawun haɗakar jam'iyyun, Alexandra Pangha, ya ce "rashin ta-ido ne a ce an rantsar da Janar Ngwema a matsayin shugaban Gabon a ranar Litinin mai zuwa kamar yadda take-taken sojojin ke nuna wa".
Har yanzu sojojin na tsare da Shugaba Ali Bongo da iyalansa a fadar gwamnati, kuma babu wani karin bayani kan halin da yake ciki ko matakin da za su ɗauka a kansa.