Wani matashi dan gwagwarma Hon Isah Muhammad Isah (Abba Kura) yana fadin hakane a wata ganawa da wakilinmu Jamilu Lawan Yakasai yayi dashi, inda yace nasarar makiyan Kano a kotu al'ummar Kano sunyi allawadai dashi, domin babu kamshin gaskiya kwata-kwata aciki.
Inda yace a yanzu haka jam'iyyar su ta NNPP tayi nisa wajen tattara dukkannin bayanai domin daukaka kara a kotu gaba, kuma suna da yakinin kotun gaba zatayi musu adalci, Abba Kura yakuma yi kira da al'ummar Kano musamman ma matasa dasu kwantar da hankulansu suke da nasara agaba.
Hon Abba Kura yace dayardar Allah sai Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf yayi shekaru takwas 8 yana kan karagar mulki, inda yace su kansu yan jam'iyyar APC sunriga sunsan al'ummar Kano basa sansu.
Ina bawa maigirma Gwamna shawarar ya gaggauta cire dukkan ciyamomi yanada kantomomi domin karya kashin makiya kano.
A karshe Abba Kura yace yan sushiyal midiya sucigaba da tallata ayyukan gwamnatin Kano, bangaren shari'a kuma suyita addu'oi neman nasara tare da addu'oin alkunut akan zaluncin da akai musu.