Dan Majalissar Kura da Garun Malam mai wakilatar su a Majalissar Dokokin Jihar Kano Mai Girma Hon. Dr Zakariyya Alhassan, yasamu damar ziyartar masu kasuwanci kayan gwari da suke kasuwancin su a Jahar Legas wato yen mill 12 market da sauran su Na Kura da Garun Malam Domin Ganin Yada Suke Gudanar Da Kasuwan Cinsu.
A yayin ziyarar tasa ya nuna jindadinsa dayaga masu kasuwancin gwarin suna kasuwancin su cikin tsari da kwanciyar hankali,
Ya kumayi musu alkawarin basu dukkan goyon bayan da suke bukata daga bangarensa.