Haka kuma kotun ta ayyana Natasha Akpoti-Uduagan ta jam'iyyar PDP a matsayin wadda ta lashe zaɓen da aka gudanar cikin watan Fabrairu.
Jagoran kotun Mai shari'a K. A Orjiako ya ce an ƙara wa Ohere ƙuri'u a rumfunan zaɓe tara cikin ƙaramar hukumar Ajaokuta, yayin da kotun ta ce an rage wa Natasha ƙuri'u da gayya a hukumar zaɓen da kuma wasu rumfunan zaɓe uku da ba a shigar wa Natashan ba a ƙaramar hukumar.
Bayan da kotun ta kammala tattara alƙaluman ne ta ayyana Natasha ta jam'iyyar PDP a matsayin wadda ta yi nasara a zaɓen bayan da kotun ta ce ta samu ƙuri'a 54,074, yayin da ta ce Sanata Ohere ya samu kuri'a 51,291.