Wanda Hon Hayatu Musa Dorawar Sallau na jam'iyyar APC ya shigar akan kalubalantar nasarar da hukumar INEC ta tabbatar ga Hon Dr Zakariyya Alhassan, inda yayi zargin cewar abokin hamayyarsa na Jam'iyyar NNPP yayi ingizon kuri'u hadi da fasa akwatunan zabe a lokacin gudanar da babban zaben daya bawa jam'iyyar NNPP nasara.
Sai dai bayan jin kowanne bangare kotun sauraren karar zabe ta yanke hukunci a wannan rana ta Asabar Talatin Ga Watan Satumbar Shekara Dubu Biyu Da Ashirin Da Uku 20-09-2023, inda kotun ta kori wannan kara haka zalika taci tarar Hon Hayatu Musa Dorawar Sallau na Jam'iyyar APC mai kara kudi har Naira Dubu Dari Shida N600,000 Kamar yadda lauyan dayake kare wanda ake kara Barr Tajuddeen Shitu ya bayyanawa wakilinm Jamilu Lawan Yakasai bayan kammala yanke hukunci.