Majalisar dokokin Jihar Kano ta amince da a gayyaci Salisu Auwalu yaron da ya tsinci kudi a Babur din Adaidaitansa bayan ya sauke wasu fasinjoji guda biyu.
Dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Doguwa Hon. Salisu Ibrahim Muhammad ne ya kawowa majalisar labarin irin halayya ta gari da Yaron da Iyayensa suka nuna wajen mayar da kudin da dansu ya tsinta a babur dinsa duba da halin matsananciyar rayuwa da suke ciki.
Ya zuwa yanzu dai Salisu Auwalu Yana Shan yabo ta bangarori daban daban na Jihar nan da suran jihohi dama wasu daga cikin kasashen dake makwabtaka da Najeriya.
Daga karshe wakilinmu na majalisar dokokin Jihar Kano Abdullahi Ibrahim Doguwa ya ruwaito mana cewa Salisu Auwalu zai zo majalisar ne domin Kakakin majalisar Hon.Jibril Ismail Falgore da sauran Yan uwansa Yan majalisa su gaisa Daya bayan,bisa wannan hali na a yaba da Dan asalin Jihar Kano yayi.