Kevin McCarthy ya ce binciken zai mayar da hankali ne kan zarge-zargen "saɓa ƙa'idar aiki, kawo cikas wurin aiki da kuma rashawa."
Ƴan majalisa na jam'iyyar Republican sun kwashe lokaci suna bincike kan Biden tun bayan da suka ƙwace iko da zauren majalisar a watan Janairu.
Ba a dai samu Biden da wani laifi ba takamaimai tun bayan fara bincike-binciken.
Wannan ne mataki na farko a tsarin da za a bi wanda zai iya kai ga batun kaɗa ƙuri'a kan tsige shugaban a Majalisar Wakilai ta ƙasar.
A wani saƙo da ya fitar a ginin majalisa na Capitol, Mr McCarthy ya ce "akwai ƙwararan hujjoji kan zarge-zargen da ake yi wa shugaban ƙasar."
Yanzu haka dai ana binciken ɗan shugaban ƙasar, Hunter Biden bisa zargin saɓa wa dokar biyan haraji a harkar kasuwancinsa.