Zeine ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai da ya kira 'yan mintuna da suka wuce a birnin Yamai, yana mai cewa amma har yanzu ba a cire takunkuman da aka saka musu ba.
"Abubuwan da suka nema su ne tattaunawa da Ecowas, da ganin shugaban ƙasa [Bazoum], da kuma saka lokacin da za a mayar da mulki ga farar hula," in ji shi.
"Tsohon shugaban Najeriya da sarkin Musulmi sun zo nan sau biyu, manyan malamai ma sun zo. Kuna gani ni na raka su suka ga Bazoum.
"Sannan mun ce musu [wa'adin miƙa mulki] ba zai wuce shekara uku ba kuma lamari na al'ummar ƙasa - saɓanin yadda ake faɗa a kafofin yaɗa labarai, ba shekara uku muka ce ba."
Ya kira takunkuman da Ecowas - ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma - ta saka wa Nijar ɗin a matsayin "haramtattu" sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yuli.
Ya bayyana cewa suna fatan nan da makonni masu zuwa za a cimma matsaya tsakanin sojojin mulkin ƙasar da kuma Ecowas.