Zababben Dan Majalissar Jiha na Kura da Garun Malam Hon. Dr Zakariyya Alhassan ya aike da bukatar sake sabbinta wasu hanyoyi ga Kwamishinan Raya Karkara da birane ta Jihar Kano. Hon. Hamza Sufiyanu Kachako.
Hanyoyin sun hada da..
1- hanyar da ta tashi daga cikin Garun Malam Zuwa Lanjan.
2- hanyar yashi Zuwa Zango (mazabar Jobawa)
3- hanyar Garun malam Zuwa Dan Maura.
4- Garun Malam Zuwa Yadakwari.
5-Bakin asibitin Dukawa Zuwa Babban Gida (Mazabar dukawa).
6- titin yakasai dake Karfi Zuwa Kura.. (mazabar Karfi Kura)
Da yake bayyanawa wakilinmu Jamilu Lawan Yakasai Dan Majalissar yace wadannan hanyoyi sun lalace, kuna suna bukatar a gaji shiyasa yaga da cewar sabbinta titinan.