Rahotanni na bayyana cewa a yanayin da ake ciki a yanzu matsalar tsaro ta kai bango a Wanke da Magami da 'Yar Tasha da Dan Sadau da Dan Kurmi da dai sauran sassa a jihar Zamfarar.
Kuma galibin mazauna waÉ—annan kauyuka na cewa suna ciki hali na ni 'ya su saboda azaba da hannunsu sakat da bindiga ke yi.
Wani magidanci da BBC ta tattauna da shi ya ce ''Ba ka isa ka taso daga gusau ka nufi magami ba, ba tare da rakiyar 'yan sa kai ko sojoji ba.
"Idan ka taso daga Gusau sai ka sauka a wani gari da ke kan hanya ka yi kwanaki amma tsakanin Magami da Janguma kilomita 25, amma rashin tsaro ya sa duk wanda ya bi wannan hanya sai ya yi bara''.
Matsalar tsaro ta nakasa harkokin noma a Zamfara'
Rashin fita gonaki da 'yancin noma na daga cikin abubuwan da suka sake raunata waÉ—annan mutane da ma kauyukansu.
Monaman da BBC ta tattauna da su na cew basu da ikon yin tafiyar kilomita guda daga garin Magami za a sace mutum ko a harbe shi.
''Yanzu haka mutanen garin Magami da ke tsare a gurin 'yan fashin daji sun kai 20, wasu ba za su dawo da rai ba, in ji manomin da ya buƙaci a sakaya sunansa.
"Sannan wasu kuma in an ce a biya kuÉ—in fansa kafin a sako su 'yan uwansu basu da kuÉ—in da za su biya, mutane su na kwashe kwanaki biyu a jere ba su ci abinci ba".
Manoma ya ce a halin yanzu haka mata da yawa sakin aurensu ake yi saboda rashin abinci, yayin da yara kanana suka koma bara.
"Akwai kuma wasu matan da yanzu haka dusar awara suke amfani da ita a matsayin abinci saboda tsananin yunwa".
Mazauna garuruwan da suke makotaka da Magami sun bukaci gwamnati ta fara daukar matakan tsaro kan hanyoyin Magami zuwa Gusau da Magami zuwa É—an Sadau da kuma Magami zuwa dan Kurmi, ta hanyar yiwa jami'an tsaro sansani a gurin don walwalar al'ummar da 'yan kasuwa ta dawo.
Kakakin gwamnan Zamfara Sulaiman Bala Idris ya shaida cewa ana bin matakan da suka kamata domin magance wannan al'amari.
A cewarsa gwamnan jihar, Dauda Lawal ya zauna da shugabannin tsaro na jihar kuma ya gabatar musu da irin bala'in da al'umma suke ciki.
Gwamnan ya na sane da cewa kullum sai 'yan fashi sun tare waɗannan hanyoyi, don haka ya buƙaci su aika jami'an tsaro su dinga sintiri da motoci masu sulke domin samar da zaman lafiya.
Jihar Zamfara dai na É—aya daga cikin jihohin Najeriya da matsalar tsaro ya yi wa katutu a tsawon shekaru.
BBC