Gwamnati ta musanta waɗannan labarai. "Muna tabbatarwa da mutane babu wani abun tashin hankali kuma muna ba su shawarar kowa ya koma ya ci gaba da harkokinsa na yau da gobe," kamar yadda kakakin gwamnati Thierry Moungala ya wallafa a shafin X da a baya aka fi sani da Twitter.
Juyin mulki a yankin Yammacin Afrika na neman zama ruwan dare a 'yan shekarun nan.
Sojoji ne ke shugabantar ƙasashen Mali da Burkina Faso da Guinea da Nijar da kuma Gabon, suna kafa hujja da cewa shugabannin da suka hamɓarar sun gaza kawo ƙarshen matsalar tsaro musamman a ƙasashen yankin Sahel.
Congo Brazzaville ba ta cikin yankin Sahel, inda barazanar masu jihadi iƙirarin jihadi ta zama jiki, kuma wataƙila wannan raɗe-raɗin ya samo asali ne saboda daɗewar shugaban ƙasar na yanzu a kan mulki, inda ya jagoranci ƙasar a tsakanin shekarar 1979 zuwa 1992 sai kuma ya cigaba daga 1997 har ya zuwa yanzu.
Ana sa ran Shugaba Denis Sassou-Nguesso zai halarci taron MDD na 78 wanda za a yi a Amurka daga ranar 18 zuwa 19 ga watan Satumba.