Jam'iyyar adawar ƙasar ta bayyana zaben da ya ba shi nasara da marar inganci, ta kuma ce shugaban ba zai iya kare kansa kan jerin sunayen ministocinsa ba.
An naɗa ɗan shugaban ƙasar, David Kudakwashe a matsayin ƙaramin ministan kuɗi.
Ya kuma naɗa ɗan yayansa, Tongai Mnangagwa a matsayin ƙaramin ministan yawon buɗe ido.
Wani jami'in ƴan adawa, Fadzayi Mahere ya bayyana majalisar ministocin a matsayin cakuɗuwar mutanen da ba su cancanta ba, da gurɓatattun mutane da kuma waɗanda aka naɗa saboda son kai.