Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, ta kori ƙarar Ɗan takarar jam'iyya hamayya ta PDP Atiku Abubakar, da ke ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu na jam'iyyar APC.
Gabanin wannan sai da kotun ta fara watsi da ƙarar Peter Obi ɗan takarar jam'iyyar LP wanda ya zo na uku a zaɓen 2023.
An shafe yini guda ana sauraren hukunci kan wannan ƙararraki.
Tuni dai Shugaba Tinubu ya yi maraba da wannan hukunci, cikin wata sanarwa da ya fitar mai dauke da sa hannun mataimakinsa na musamman kan harkokin 'yaÉ—a labarai Ajuri Ngelale.