Haka kuma Tinubu ya amince da naɗin Mr. Ayodele Olawande a matsayin ƙaramin ministan matasa.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce za a tura sunayen mutanen biyu zuwa majalisar dattawan ƙasar domin tantance su.
Dakta Jamila Bio Ibrahim - matashiyar likita - a baya-bayan nan ta riƙe muƙamin shugabar mata ta matasan jam'iyyar APC mai mulki.
Ta kuma riƙe muƙamin babbar mai taimaka wa gwamnan Kwara kan cimma muradun ƙarni.
Shi kuwa Mista Ayodele Olawande shi ne shugaban matasa na jam'iyyar APC.
A baya-bayan nan ya yi aiki a ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin ƙirƙire-ƙirƙire daga 2019 zuwa 2023.