Sanata Kashim Shettima ya ce matakin wani yunƙuri ne na magance matsalar tsaro da yankunan ke fama da ita.
Yana wannan jawabin ne a lokacin da Majalisar Ƙoli kan Harkokin Addinin Musulunci - ƙarƙashin jagorancin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar lll - ta kai ziyara fadar shugaban ƙasar.
Tun da farko shugaban ƙasar Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da ke haifar da matsin rayuwa da gwamnatinsu ke yi, sakamakon cire tallafin man fetur za su amfani 'yan ƙasar da dama a nan gaba.
Tinubu ya ce yana da yaƙinin sauye-sauyen za su amfani 'yan ƙasar a nan gaba musamman a fannonin Ilimi da ayyukan yi da lafiya da abubuwan more rayuwa.
“Najeriya ta É—auki alÆ™awari, kuma sauye-sauyen za su kawo mana ci gaba mai É—orewa, za mu gina Æ™asarmu, ta yadda 'ya'yanmu za su yi alfahari da ita", in ji shugaban Æ™asar.
Shugaban ya shaida wa majaliar ƙolin cewa gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da gwamnatocin jihohi domin bunƙasa harkokin noma da kiwon dabbobi, domin fara fitarwa zuwa ƙasashen ƙetare, lamarin da zai samar da ayyukan tare da samar da kudin shiga ga ƙasar.