Kamar a yawancin kasashen Afirka ana kallon luwadi a matsayin laifi da rashin É—a'a a Najeriya.
Ƙasar dai na da tsauraran dokoki na hana auren jinsi ɗaya.
Lauyan da ke kare mutanen ya ce za a bayar da belin su amma sai ya miƙa wa kotu kuɗi kwatankwacin dalar Amurka 600 a kan kowanne ɗaya daga cikin mutanen da aka tsare.
Ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta soki ‘yan sandan Najeriya kan yadda suka gabatar da waÉ—anda ake zargin a gaban ‘yan jarida a bainar jama’a tare da yi musu tambayoyi kan zargin da ake musu.
Duk da Allah wadai da kasashen duniya suka yi, an kafa dokar a ƙasa da shekaru 10 da suka gabata da ta haramta auren jinsi ɗaya a bainar jama'a tare da hukuncin daurin shekaru 10 da kuma shekaru 14 ga duk wanda aka samu da laifin yin auren jinsi.
A shekarar 2019 ‘yan sanda a jihar Legas sun gurfanar da wasu mutum 47 a gaban Æ™uliya amma kotu ta yi watsi da Æ™arar saboda ‘yan sanda sun kasa bayyana da kuma gabatar da shaidu.