Wani matashi ya rasa 'yan yatsu a wani kamfani anan Kano yayin da yake tsaka da aiki
Matashin mai suna Awaisu Yahaya, yace 'yan yatsunsa sun guntele ne a lokacin da yake gudanar da aiki a Kamfanin 5 Star dake Sharada.
Tsawon shekara biyu matashin yana neman kanfanin ya samar masa da makoma a rayuwarsa amma abin ya gagara
Kafar Arewa Radio ta rawaito cewar ta tuntubi kamfanin, sai dai kamfannin sun bayyana cewa sunyi masa tayin Naira dubu dari biyar amma ya raina, sannan suna shirin bashi miliyan guda tare da bashi damar cigaba da aiki da baida wahala.
Ku cigaba da bibiyarmu domin kawo muku matsayar da za'a cimma.