Bugu da ƙari sallamar ta shafi mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin wasanni da matasa,Yusuf Imam, wanda aka fi sani da Ogan Boye wanda shi ma ake zargi da furta kalaman da ba su dace ba a madadin gwamnatin.
A ƙarshen makon nan ne bidiyon jami'an gwamnatin suka rinƙa yawo a shafukan sada zumunta, inda suke furta kalamai game da shari'ar da ake yi kan zaɓen gwamnan jihar da ya gabata.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Baba Halilu Ɗantiye da kuma na shari'a Haruna Isa Dederi suka karanta a daren ranar Alhamis, sun ce jami'an gwamnatin sun yi magana ba tare da izinin gwamna ba, sun kuma yi kalamai na tunzura al'umma sannan kuma sun ci zarafin mataimakin shugaban ƙasar, Kashin Shettima.
A cikin kwanakin nan dai yanayin na siyasa ya ƙara zafafa gabanin hukuncin kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamna na jihar.
Manyan jam'iyyu a jihar, NNPP da APC sun gudanar da addu'o'i da azumi domin neman nasara a shari'ar.
A baya dai ɗaya daga cikin alƙalan kotun ta yi zargin cewa akwai wasu da ke yunƙurin bai wa alƙalai da lauyoyin kotun cin hanci domin samun nasara a shari'ar.