Mai shari'a Haruna Tsammani ne ya gabatar da hukuncin, yayin dogon zaman kotun a ranar Laraba.
Kotun dai ta yi watsi da manyan ƙorafe-ƙorafe guda uku da Peter Obi da kuma jam'iyyarsa ta LP suka shigar. Shi ne hukuncin ƙara ta biyu a cikin uku da kotun take zaman yankewa a ranar Laraba.
Atiku Abubakar, jagoran adawa na Najeriya, da Mista Peter Obi, ɗan takarar da ya zo na uku da kuma jam'iyyar APM, duka suna ja da sakamakon da ya bai wa Bola Tinubu nasara a zaɓen.
Alƙalan kotun biyu Mai shari'a Haruna Tsammani da takwaransa Mai shari'a Abba Mohammed sun kwashe sama tsawon sa'a biyar suna karanta hukuncin ƙarar Peter Obi.
Yayin gabatar da hukuncin alƙalan kotun biyar, kotun ta yi watsi da bahasin shaidu guda 10 cikin 13 da ɗan takara Peter Obi da jam'iyyar LP suka gabatar.
Haka kuma, Mai shari'a Tsammani ya ce kotun ta ƙi amincewa da iƙirarin masu ƙorafi na cewa an yi aringizon ƙuri'u a jihohi irinsu Yobe da Oyo da Kano da sauransu, saboda ba su gabatar da bayani a kan tasoshin zaɓen da al'amarin ya faru ba.
"Hankali ba zai ɗauka ba cewa, mai ƙorafi ya yi zargin maguɗi a wurare masu yawa cikin tasoshin zaɓe 176,000 da mazaɓu sama da 8000 na ƙananan hukumomi 774 a cikin jiha 36 da kuma Abuja, amma ba tare da ya zayyana taƙamaimai wuraren da aka yi maguɗin da ya yi zargi ba," kotun ta ce.
Hukuncin ya kuma ce jam'iyyar LP ta gaza kafa hujja kan iƙirarin da ta yi, na samun kura-kurai a zaɓen watan Fabrairu.
Jam'iyyar ta yi zargin cewa hukumar zaɓe ta INEC ta rage mata ƙuri'un da ta ci, inda ta ƙara a kan ƙuri'un jam'iyyar APC, sai dai a cewar kotun, jam'iyyar LP ta gaza gabatar da cikakken bayani a kan haƙiƙanin yawan ƙuri'un da ta ci, kafin a rage mata su, kamar yadda ta yi iƙirari, kuma ba su iya ba da bayani a kan tashoshin zaɓen da hakan ta faru ba.
Sai dai, kotun ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar APC ba ta da hurumin ƙalubalantar matsayin Peter Obi na kasancewarsa, ɗan jam'iyyar LP.