Ma'ana alƙalan kotun ba su samu halartar harabar kotun da kansu ba.
Sai dai lauyoyi da wakilan jam'iyyun da lamarin ya shafa suna zaune a cikin kotun inda suke kallo da sauraron hukuncin ta majigi.
Ya zuwa yanzu dai babu masaniya kan dalilan da suka sanya alƙalan suka gaza halartar zaman da kansu a harabar kotun da ke cikin birnin Kano.
Sai dai kafin ranar yanke hukuncin al'amuran siyasa sun yi zafi tsakanin magoya bayan manyan jam'iyyu biyu, APC da NNPP, da ke hamayya da juna a jihar.
Kuma a baya babbar alƙaliyar kotun ta koka kan yadda wasu ke yunƙurin bai wa kotun cin hanci domin samun nasara.