Shinkafa na cikin kayayyakin da gwamnatin Najeriya ta haramta shigar da su a shekarar 2015 cikin kasar a wani mataki na kokarin bunkasa noma a kasar da nufin dogaro da kai.
Kungiyar masu sarrafa shinkafar ta cikin gida, ta ce matakin dage haramcin babbar barazana ce bayan sun zuba makudan kudi a kasuwancin.
Shugaban kungiyar, Peter Dama, ya shaida wa BBC cewa, a gaskiya wannan mataki ya zame musu kamar bala’i ne domin gwamnati ta sanya sun sanya kudadensu sun sayi kayan sarrafa shinkafa, sannan an sa jama’a sun shiga noma shinkafar, ga shi jama’ar kasa sun fara son shinkafar da ake samarwa a gida, "sai kawai mu ji an ce an dage haramcin shigo da shinkafar waje."
Ya ce, “ Wannan mataki na gwamnati ya kawo mana cikas, ga shi kuma zai sa a rufe kamfanoni da dama, sannan jama’a da yawa za su rasa aikin yi ga shi kuma manoma da dama kuma ba za su yi aikin shinkafa, kuma sannan za a fara shigo mana da shinkafar da ta riga ta rube.”
Peter Dama, ya ce: ‘’Gwamnati ba ta shawarce mu ba kafin ta dauki wannan mataki, kuma batun cewa shinkafar da ake samarwa a gida ma tana tsada ai kowa ya san ba da ruwa ake nomata ba, kuma yadda ake noman nata ma ai sai a duba a gani, sannan wajen ban ruwa ba wasu da kananan inji suke yi kuma ai da man fetur ake amfani a injin, kuma kowa ya san tsadar mai a yanzu.”
Shugaban ya ce babbar damuwarsu idan har aka fara shigar da shinkafar waje to mutane sai su koma kanta domin su al’ummar Najeriya idan aka ce musu ga wani abu na waje ko da ruwan sha ne sai hankalinsu ya koma kansa.
Ya ce, “ Mu mun yi iya bakin kokarin mu wajen nunawa ‚yan Najeriya cewa shinkafarmu ta gida ta fi afki sannan ta fi amfani a jiki domin mu ta mu ba a ajiye ta ta yi shekara da shekaru ba.”
“ Mu ba ma yi wa shinkafarmu ta gida doguwar ajiya.”
Ya ce, "A yanzu mu matakin da za mu dauka shi ne za mu yi magana da gwamnati mu ba ta shawara, sannan mu saurara mu ji ko za su saurari kokenmu.”
Peter Dama, ya ce,” Idan har ana so a samu saukin tsadar shinkafa a kasa to sai a rage kudin man fetur da na kayan aikin gona, da kuma ba wa manoma taimakon da zai bunkasa nomansu.”