Babu abinda yafi karfin Ubangiji domin mu a wajensa muke nema kuma mundogara dashi kuma bazai barmu mutabe ba, za'a dawo musu da Alh. Abba Kabir Yusuf domin cigaba da kawo ayyukan more rayuwa a fadin Jihar Kano.
Comr Mamunu Takai yace duk wata nasara bata iya zuwa kai tsaye batare da fuskantar kalubale ba, inda yace wannan jarabta da Allah yayi musu wanda kotu ta kwace nasarar su tabawa jam'iyyar hamayya hakan ba yana nufin cewa tatafi bane.
Suna da yakinnin Allah zai dawo musu da ita kuma su sami albarka fiye da wacce sukai na kwanaki Darin 100 Gwamna Alh. Abba Kabir Yusuf, inda yakara da cewar shi zalunci baya zuwa ko ina, kuma Allah ya gaggauta karbar addu'ar duk wanda aka zalunta.
Domin anzalunci al'ummar Kano a cewarsa, shiyasama yake kara kira ga al'ummar Takai dama Jihar Kano cewar duk wanda yake gannin anzalunce ya gaggauta kai kokensa wajen Allah (S.a.w) domin yabi masa hakkinsa.
A karshe Comr Takai yace jam'iyyar su na nan nahada duk wasu hujjuji domin mikawa kotun daukaka kara, domin bawa al'ummar Kano abinda suka zaba Alh. Abba Kabir Yusuf