Kwamared Kabir Dakata Jigone a Kungiyar fafutuka da samarwa al'umma shugabanci na gari wanda ake kira (KAJA), ya bayyana cewa mahangar da dangane da batun shari'ar Gwamnan Kano.
Inda yace Matsayin Barr. Audu Bulama Bukarti da Barr. Abba Hikima Fagge akan shari'ar zaben Kano.
Tun kafin a yi shari'ar Kano Barr. Abba Hikima Fagge na da tunanin cewar za a iya ayyana zaben a matsayin inkwankulusib ma'ana wanda bai kammala ba sabo da banbancin da ke tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Nasiru Gawuna bai kai yawan kuri'un akwatinan da aka soke zabensu. Shi ma Barr. Bukarti wannan shi ne tunaninsa.
Kwamared Kabir Dakata da ya karance matsayin INEC akan wannan lamarin sai ya fahimci babu inkwankulusib domin ita INEC ta na la'akarine da adadin wadanda su ka karbi katinan zabensu ba wai adadin wanda su ka yi ri rijista ba.
A sabo da haka, shi Gwamna Alh. Abba Kabir ya ci zabensa babu batun inkwankulusib.