Ministar Jinkai da Walwala Dr Betta Edu ta fitar da sanarwar dakatar da shirin na N-POWER domin a gudanar da binciken akan yadda ake zargin an saka sunayen mutane, da yadda ake zargin fitar da makudan kudade da zummar ana rabawa al'umma da kuma fitar da masu Certificate na bogi, da ma waÉ—anÉ—a kwata-kwata ba su cancanta ba.
Gwamnatin baya data shude ita ce ta kirkiro shirin N-POWER domin ragewa 'yan kasa radadin talauci, hakan yasa Gwamnatin Buhari tace zata runga diban masu sha'awar ayyuka a fannuni daban-daban na hukumomin Gwamnatin domin dogaro da kai.
Sai dai wannan dama ta ta'allakane gawanda yayi karatun boko, kuma shi wannan aiki na wucin gadine, da ake biyan mutum Kudi Naira Dubu Talatin N30,000 ko wanna karshen wata, kamar dai yadda ake biyan jami'an Gwamnati albashib su.