Shugaban hukumar gidan gyaran hali da tarbiyya na jihar Katsina, Muhammad Abdulmumini Haruna, ya tabbatar da guduwar wasu matasa biyu "2" waɗanda kotu ta aika da su gidan gyaran hali domin jiran shari'a waɗanda ake zargin yan fashi da makami ne tare da satar motocin mutane a cikin birnin jihar Katsina.
Wata kafar watsa labarai ta rawaito cewa ko a ƙwanakin baya, an zargi ɗaya daga cikin matasan da suka gudu daga gidan yarin mai suna Ibrahim Lawal wanda aka fi sani da Abba Kala, cewa ya taɓa amfani da wayarsa ya tsara yadda aka saci duk da kuwa yana tsare a gidan.
Sai dai al'umma da dama suna zargi wasu daga cikin ma'aikatan gidan yarin da haɗa baki da Abba Kala domin kuɓutar da su daga gidan gyaran halin kamar yadda Jakadiya ta ruwaito.
A cewar shugaban gidan gyaran halin na Katsina, Ƙwantirola Muhammad Abdulmumini, ya shaida wa manema labarai cewa ana kan bincike kan guduwar matasan domin kamo su a duk inda suka shiga tare hukunta duk wani jami'i da aka samu yana da hannu cikin guduwarsu.