Dakarun Jami'an Tsaro na sakai da Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙaddamar “KSCWC sun samu nasarar ceto wasu shanu da ƴan bindiga suka sace a garin Ƙanƙara da ke jihar Katsina.
Wata kafar watsa labarai ta Katsina Reporters ta rawaito cewa Jami'an tsaron sakan sun ceto shanun ne a wani harin ƙwantan ɓauna da suka kai a dazukan garin Ƙanƙara.
Cikin watan da muke ciki ne Gwamnan Jihar Katsina ya kaddamar da wannan runduna domin kakkabe masu garkuwa da suka addabi Jihar Katsina.