Zababben Dan majalissar Jihar Kano na yankin Kura da Garun Malam kuma shugaban kwamatin Lafiya a Majalisar Jihar ta Kano Hon Dr. Zakariyya Alhassan ya gabatar da Kudirin yin garambawul tare da gina babban bangaren Gwaje-Gwaje (DIAGNOSTIC) a babban asibitin Kura (General Hospital)dake kan titin zuwa Zariya.
Mun sani Cewa: asibitin General hospital babban asibiti ne da Babu kamar sa akan titin Zaria Road idan ka baro Zaria wanda Sama da local government 10 ne ke amfani da wannan asibiti.
Bayan kammala kai wannan koke da Dan Majalissar yakewa majalissar ne, wakilin mu Jamilu Lawan Yakasai yasamu ganawa da Dan majalisar, inda yayi masa karin haske da cewar wannan Asibiti shine babban asibiti a wannan karamar hukuma.
Inda yace rashin infanta wannan bangare yasa alatillas al'ummar suke zuwa asibitocin cikin birni, ga kuma yanayi da ake ciki na matsanancin yanayi na karancin kudi a hannun al'umma, kudin magani kawai yana gagarar jama'a balle takai da cewar kudin mota da dai sauran abubuwa.