Mutane da dama sun shiga rudani tare da yin mamakin haihuwar Jaruma Rahama Mk matar Gwamnan shirin kwana chassa'in kuma sabuwar Gwamnan a shirin wacce take amsa suna da Hajiya Rabi mata ga Bawa mai kada.
Inda wasu suke tambayar kansu cewa, dama tana da aure ne? yayin da wasu suke tambayar kansu kuma tana da aure amma mijinta ya kyale ta tana yin Wasan Kwaikwayo?
Amsa itace Eh, tabbas tana da aure, saboda haka yaron data haifa 'Dan Sunnah ne kamar kowa da aka same shi ta hanyar aure,
Sannan maza iri-iri ne, akwai wanda yana da saukin kai sosai kuma ba shi da kishi sosai koda kuwa yana matukar son wannan matar tasa.