Wata takardar kotu mai kwanan watan 2 ga watan Oktoban 2023, ta nuna cewa Gwamna Abba Kabir ya zayyana Hukumar zaɓe ta INEC da jam'iyyar APC da kuma jam'iyyarsa ta NNPP, a matsayin waɗanda yake da ƙorafi a kansu.
Mai ƙorafin a cewar takardarn kotun, bai gamsu da hukuncin alƙalan kotun ƙararrakin zaɓen gwamnan Kano ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Oluyemi Akintan-Osadebay ta yanke ba.
Kotun dai ta soke ƙuri'a 165,633 daga cikin 1,019,602 da aka kaɗa wa Abba Kabir Yusuf a zaɓen 18 ga watan Maris, bisa hujjar cewa ba halattattun ƙuri'u ba ne, saboda ba su da hatimi da kwanan wata.
Don haka, kotun ta ayyana Nasir Yusuf Gawuna a matsayin halastaccen gwamna, ta kuma umarci hukumar zaɓe ta janye shaidar cin zaɓen da ta bai wa Abba Kabir Yusuf tun da farko, sannan ta bai wa Gawuna shaidar nasara.
Sai dai Abba Kabir a yanzu ya ƙalubalanci matakin, inda ya yi iƙirarin cewa hukuncin ƙaramar kotun cike yake da kura-kurai, har ma ya kafa hujjoji guda 43.
Cikin buƙatun da gwamnan na jam'iyyar NNPP ya nema a gaban kotun ɗaukaka ƙara, har da ta neman jingine hukuncin kotun sauraron zaɓen gwamnan Kano, sannan ta kori ƙarar da jam'iyyar APC ta shigar tun da farko.
Tun farko, bayan yanke hukuncin na ranar 20 ga watan Satumba, ɓangaren jam'iyyar APC ya faɗa wa BBC cewa ba sa fargaba a kan zuwa kotun ɗaukaka ƙara.