Cif Wole Olanipekun, SAN ne zai jagoranci karar Gwamna Abba Kabir akan hukuncin da kotun Kano ta yanke.
Wole yana daya daga cikin Kwararrun lauyoyi a Najeriya.
Ya jagoranci daukaka karar Nyesom Wike. Ya jagoranci tawagar lauyoyin Marigayi Umaru Musa 'Yar Adua wajen samun nasarar kare kura-kuran zaben 2007 inda suka samu nasara a kotun koli da ci 4-3.
A 2011 ya kare nasarar GEJ a Kotun Koli. Ya ba wa Buhari shawarwarin shari’a a lokacin batun takardar shaidar Karatunsa, kuma ya jagoranci karar da Tinubu ya yi wa Atiku Abubakar, tare da jagorantar tawagarsa da suka yi watsi da karar sa na CCT.
A kwanakin baya ne kamfanin MTN ya dauke shi aiki domin ya jagoranci tawagarsu ta lauyoyin da ke kalubalantar tarar da hukumar ta NCC ta ci ta yi duk da cewa shari’ar ba ta zuwa kotu.