Gwamnan Jihar Kano Alh. Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnnin a gaggauta gyara Asibitin Sir. Sanusi General Hospital a kokarin sa na kara bunkasa harkokin kiwon lafiya.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wata ziyarar ba-zata da ya kai asibitin.
Gwamnan wanda ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda asibitin ya lalace, ya yi alkawarin cewa za a fara aikin gyaran ne domin tabbatar da majinyata da ma’aikatan lafiya sun samu yanayin da ya dace a asibitin.
Ya kuma yi wa marasa lafiya dake asibitin fatan samun sauƙi, sannan ya bada kyautar naira dubu ashirin ga kowanne mara lafiya dake asibitin a matsayin tallafin gaggawa.