Gwamnan Jihar Kano Alh. Abba Kabiru Yusuf zai biya ƴan fansho kimanin mutum Dubu Biyar 5000 gratitude da suke bi cikin sati mai zuwa.
Inda Gwamnatin ta ware kudi kimannin Naira Biliyan Shida domin fara rage hakkokin tsaffin jami'an Gwamnatin da suka shafe shekaru suna hidimanta mata.
Gwamnan ya bayyana haka a wajen rufe taron bita ga kakakin hukumomin Gwamnatin Kano wanda aka shafe yini uku anayi,
A kwanakin da suka gabatane Gwamnan ya biya iyalan mamata Kudin Gratitude din su.
Ma'aikatan Jihar Kano sundade suna fargabar kammala aikinsu wanda suke cewa hakkokinsu basa fitowa sai sunbada nagoro kamar yadda wani ma'aikaci ya bayyana wa wakilinmu Jamilu Lawan Yakasa,
Inda yace sunshafe shekaru kusan Tara 9 ba'a basu hakkokinsu ba, sakamakon rashin hanya da zasubi a basu.
Yace idan ma mutum yabi hanyar to sai yabada Kudin cin hancin kashi Goma cikin Dari 10%, Inda kowacce miliyan sai kabada Naira Dubu Dari.
Fatan dai Gwamnati zata sanya idanu wajen biyan hakkokin tsaffin ma'aikatan domin gujewa fadawa wancan halin da tsaffin ma'aikatan sukace wasunsu sunfada a baya.