Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf ua jagoranci Bikin kaddamar da rabon kayayyakin Makaranta ga Daliban makarantar Firamare da Sakandire.
Da suka hadar da Littattafan karatu da rubutu, alli, rajista, sabbin uniform, takalma, Benci, da kayan karatun Masu bukata ta musamman da sauran kayayyakin koyo da koyarwa
Wadanda Gwamnati zata rabawa dukkannin Makarantu da suke kananan Hukumomi 44 dake Jihar Kano Domin inganta harkar ilimi tare da saukakawa iyayen dalibai musamman a wannan yanayi da ake ciki na tsadar rayuwa.
A karshe Gwamnan yayi Jan hankalin mahukunta wajen bada kayayyakin cikin tsari domin kowanne dalibi yasami kayan koyo da koyarwa dan gudun fadawa fushin Gwamnatin.