Hukumar tace fina-finai da dab'i taJihar Kano, karkashin jagorancin shugabanta Alhaji. Abba El Mustapha, ta dakatar da sayar da Littafin Queen Primer tare da kira ga Malaman Makarantu da su guji amfani dashi.
Hakan ya biyo bayan wani bincike da hukumar tayi sakamakon korafe korafen da aka kawo kan yadda ake zargin Littafin na da wasu kalaman batsa, wadanda zasu iya kawo gagarumar matsala wadanda bai kamata ba ga al'umma da kuma rayuwar yara.
Daga karshe hukumar tayi kira ga malamai da kuma shugabannin Makarantu da su guji amfani da wannan Littafi don kuwa duk wanda aka hukumar ta kama dasu doka zatai aiki akan shi na basani ba sabo.