Gwamna Abba Gida-Gida ya bayyana cewar al'ummar Kano suna ransa dasu yake kwana, dasu yake tashi bisa soyayya da kauna da suke masa,
Da yake jawabi Abba Gida-Gida ya bayyana cewar
"Za kuma mu tabbatar da bullo da tsarin motocin haya da motocin bas na Amana ga matasan mu, za'a saka wasu masu tuka babur (Yan Adaidata Sahu) a cikin wannan shiri domin daukaka matsayinsu."
A bangaren ayyukan raya kasa kuwa, gwamnan ya ce ayyukan kilomita biyar na kananan hukumomi 44 da tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kaddamar a wa’adi na biyu na gwamnatin sa toni ayyukan sa sukai nisa,
Motocin da ake bukata, masu amfani da na’urorin zamani wadanda zasuyi aiki da sauran zurga-zurga sufuri a fadin Kano.
Alh Abba Kabir ya yi amfani da wannan dama wajen bayyana wasu ayyukan ci gaban da suka shafi ilimi, kiwon lafiya, noma, fadada tituna a cikin Kananan Hukumomin Jihar Kano,
Gina gada da kuma hanyoyin karkashin kasa domin saukaka zirga-zirgar ababen hawa,
Kawar da madatsun ruwa, gyare-gyaren asibitoci da makarantu. a kananan hukumomi 44 na Kano.