A lokacin da bikin auren gata ke kara karatuwa wanda Gwamnatin Kano karkashin Jagorancin Gwamnan Jahar Alhaji Abba Kabir Yusuf zai aurar da mata da maza 'yan asalin Jahar Kano.
Ta hannun Hukumar mai Umarni da kyayyawa da kuma hani da mummuna ta Hisbah, wanda Ustaz Aminu Ibrahim Daurawa ke shugabantar ta, sunfito da dokoki da ka'idoji kafin yin wannan aure.
Inda Hukumar tace yazama wajibi duk wanda zai auren ko mace ko namiji sai anmishi Gwaje-Gwaje jini dama cuttuka masu hatsari ga jama'a, bayan kwararan binciken da Hukumar tayi ta gano cewar Hisbah ta gano mata masu juna-biyu da masu cutar HIV a cikin wadanda ta tantance domin auren gata a Jihar Kano.
Haka kuma Hukumar tace ta gano masu cutar ciwon hanta inda toni ta umarci hukumar lafiya kan dorasu akan magunguna.