Hukumar zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa INEC ta fiitar da wata sanarwa da yammacin wannan rana ta Asabar Bakwai Ga Watan Satumbar Shekarar da muke ciki 07-10-2023.
Inda Hukumar ta nesanta kanta da wata Sanarwa da wani jami'inta ya fitar dake cewar " Hukumar INEC din ta janye daga bayar fa shaida a Kotun Daukaka Kara".
Inda Hukumar zaben ta bukaci al'umma da suyi watsi da waccan Sanarwa da ake yadawa,
Tana Mai cewa toni Hukumar tare da Lauyoyinta zasu suka kammala shirin kasance a Kotun domin tabbatar da hakikanin abinda suke da yakinin shine dai-dai agaban Kotun daukaka karar.
A Safiyar wannan rana ce aka wayi gari da gannin wata Sanarwa data ringa yawa a shafukan sada zumunta da cewar Hukumar zaben ta janye daga daukaka karar da za'ayi Shari'a tsakanin Jam'iyyar NNPP da Jam'iyyar APC.
Bayan hukuncin da Kotun sauraron karar za6e ta yanke a Kano, da cewar ta kwace nasarar Alh. Abba Kabir Yusuf na Jam'iyyar NNPP da Hukumar INEC ta tabbatar a matsayin wanda yalashe za6en Gwamnan Kano, inda Kotun ta tabawa Dr Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda yayi nasara.
Kuma kotun ta bawa INEC umarnnin cewar ta gaggauta janye shaidar data bawa Alh. Abba Kabir Yusuf ta kuma mayar da shaidar nasara ga Dr Nasiru Yusuf Gawuna.
Hakan yasa Jam'iyyar NNPP ta daukaka kara a Kotun gaba, domin tace itace Hukumar INEC ta tabbatar da APC ba,
Hakan yasa Hukumar zaben mai zaman kanta ta INEC tace data bayar da shaida a gaban Kotun daukaka karar domin tabbatar da sahihancin wanda ta tabbatar a matsayin wanda yaci zaben Gwamnan tunda fari.
Sai dai wannan Sanarwa zata kore labaran dake yaduwa a Kafafen sada zumunta dake cewar Hukumar baza ta bayar da Shaidar a Kotun Daukaka kara ba.