Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta ce hukuncin Kotun Koli a kan korafin da ta shigar tare da dan takararta Atiku Abubakar, akan nasarar zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babban abin tayar da hankali ne.
Ta ce ‘yan Najeriya har yanzu sun kasa fahimtar yadda kotun koli ta lamunci manyan batutuwan yin jabun takardu da tafka karya da shaidar zur, bisa doron rashin cika ka’idojin shigar da kara.
Kotun dai ta yanke hukuncin da ya tabbatar da nasarar zaben Tinubu a zaben ranar laraba 25 ga watan Fabrairun 2023.
PDP ta ce ita, da mafi yawan al’ummar Najeriya sun kadu kuma sun ji takaici tare da nuna damuwa a kan tunanin Kotun Kolin, wanda jam’iyyar adawar ta ce ta yi imani ya saba da tanade-tanaden tsarin mulkin Najeriya da kundin dokokin zaben kasar.
Sanarwar da sakataren yada labaran PDP na kasa, Onarabul Debo Ologunagba ya fitar, babbar jam’iyyar adawar ta jaddada cewa wani abin takaici ne a ce kotun koli ta gaza dabbaka tanade-tanaden doka.
A maimakon haka, sai ta yi watsi da kyakkyawan zaton mafi yawan al’ummar Najeriya wadanda ke kallonta a matsayin gidan samun adalci ta hanyar yanke hukunci a kan batun da ya yi la’akari da dokoki da al’amura na gaskiya a cikin wannan shari’a.
Ta ce da gaske ‘yan Najeriya sun yi tsammanin kotun koli za ta tabbatar kuma ta kare tanade-tanaden tsarin mulkin 1999 wadanda suka fayyace karara batun cancantar dan takara da sharadi mafi karanci da ake bukatar cikawa kafin a ayyana mutum a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar Najeriya.
“Musamman la’akari da bukatar doka ta cin kashi 25 na kuri’un da aka kada a birnin Abuja da kuma batutuwan da suka keta dokoki da tsare-tsaren zabe.”
PDP dai ta ci gaba da zargin jam’iyyar APC mai mulki da tafka almundahana da jirkita sakamakon zabe.