Mawaƙin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara, ya sanya gasar wata sabuwar waka da yayi akan shirin gwamnatin tarayya na ƙidaya da za'a gudanar a farkon shekarar 2024, inda ya bayyana muhimmancin ƙidaya ga yan ƙasa Nigeria.
Aisha Humaira wacce abokiyar aikin Rarara ce, tayi bayanin yadda ƙidayar za ta taimaka a sha'anin tsaro, tare da bayani akan yadda gasar za ta kasance da kuma irin kyaututtukan da za'a bayar ga wadanda suka shiga gasar, da suka hada da Mota, Babur da kuma kuɗi.
Sai dai kuma gasar bata samu karɓuwa ga ma'abota shafukan sada zumunta musamman TikTok ba, inda wasu jaruman dandalin ke ganin Rarara bai shiga lamarin kira ga gwamnati akan matsalar tsaro datakici taki cinyewa a Arewacin Nijeriya ba, saboda haka a yanzu shima ba zasu karɓi bukatarsa ba.