Kotu ta soke zaɓen Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna a jihar Nasarawa ta umarci hukumar zaɓen Najeriya (INEC) ta janye takardar shaidar cin zaɓen da ta bai wa Gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC.
A wani hukunci da kotun mai alkalai guda uku ta gabatar karkashin jagorancin Mai shari'a Ezekiel Ajayi, mafi rinjayen alƙalan sun ayyana ɗan takarar jam'iyyar PDP, David Umbugadu a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna na 18 ga watan Maris a jihar Nasarawa.
Alƙalan sun gabatar da hukuncin ne ta hanyar manhajar Zoom.
Wanda hakan ke nuni cewar kotunan sauraren zabe izuwa yanzu ta yanke hukunci guda uku a kafar zoom, wanda yahada da Jihar Kano wadda kotun ta karbe nasarar NNPP ta baiwa jam'iyyar APC, sai Jihar Kaduna wadda kotun tabarwa jam'iyyar APC wadda jam'iyyar PDP tashigar da karar, sai kuma Jihar Nasarawa wadda kotun ta kwace a wajen jam'iyyar maici ta PDP ta baiwa mai kara APC.