Kotun ɗaukaka ƙara (Court of Appeal) ta sake tabbatar da Hon. Sani Aliyu Ɗanlami, na Jam'iyyar APC a matsayin ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina.
Kotun ta ƙwace kujerar Hon. Aminu Chindo ne, sakamakon laifin amfani da takardun bogi wanda kotu ta same shi dasu, wajen shigar da bayanan takara,
Inda ta tabbatar da nasarar Hon. Sani Ɗanlami a matsayin halastaccen dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Katsina ta tsakiya.