Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a Sokoto ta tabbatar da nasarar sanata Aliyu Wamakko na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen sanatan Sokoto ta Arewa.
Babban abokin hamayyarsa a zaÉ“en, Mannir Mohammad Dan’Iya, na jam'iyyar PDP ne ya shigar da Æ™ara gaban kotun sauraren kararrakin zabe na Jihar,
Yana mai ƙalubalantar nasarar Wamakko, kan zargin amfani da takardun bogi, da rashin takardun shaidar karatu.
Cikin hukuncin da alƙalan kotun uku ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Josephine Oyefeso suka yanke, sun yi watsi da ƙarar, kan rashin gamsassun hujjoji daga ɓangaren mai ƙara.
A ranar Alhamis din data gabata ne dai kotun ta tabbatar da nasarar Sanata Aminu Waziri Tambuwal na PDP, a matsayin sanatan Sokoto ta kudu.
Har izuwa wannan lokaci daukacin karrakin zabe da aka gudanar a Najeriya nagaban kotuna daban-daban.