Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce hukuncin Kotun Koli na tabbatar da nasarar Ahmad Bola Tinubu a matsayin halastaccen zababben Shugaban Najeriya ’yar manuniya ce cewa anyi sahihin zabe ranar 25 ga watan Fabrairu.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Edwin Olofu, ya fitar a wannan rana ta Alhamis, Ganduje ya kuma shawarci Alh. Atiku Abubakar na Jam'iyyar PDP da takwaransa na LP, Peter Obi, da su yi hakuri su kara tarawa a shekarar 2031,
Lokacin da Shugaban Kasa Ahmad Tinubu zai kammala wa’adinsa na biyu.
Ganduje ya kuma taya Shugaba Tinubu murnar yin nasara a gaban Kotun Koli, inda ya ce hukuncin ya kawo karshen dukkan wata takaddamar tafka magudi da ’yan adawa ke zargin an yi a zaben shekarar 2023.
Abdullahi Ganduje ya kuma ce hukuncin zai bawa Tinubu damar mayar da hankali wajen farfado da manufarsa ta farfado da Najeriya wacce jam’iyyarsu ta sa a gaba
Daga nan sai ya bukaci ’yan takarar da su karbi kaddara sannan su zo su hada gwiwa da gwamnatin Tinubu wajen kai Najeriya tudun mun tsira.
Shugaban na APC ya kuma roki ’yan Najeriya ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba da su ci gaba da mara wa Gwamnatin Tinubu baya har ya kai ga cim ma kudurorinsa na alheri ga kasar.